Gane Mini Hanya: Tare da ministan tsaron Najeriya Badaru Abubakar
Gwamnatin Najeriya ta jaddada cewa ana samun gagarumar nasara a yaki da matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar.
Wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta lashi takobin magance matsalar yayin da ta cika shekara biyu a kan Mulki.
Sai dai duk da iƙirarin gwamnatin, har yanzu ana samun rahotannin kai hare-hare a sassa daban-daban na ƙasar da ke fama da wannan matsala, lamarin da ya janyo mutuwar mutane fiye da17,000 a cikin waɗannan shekaru biyu, a cewar alkaluman kamfanin tsaro na Beacon Consulting.
A filinmu na Gane Mani Hanya na yau, Imam Saleh ya tattauna da ministan tsaron Najeriyar, Muhammad Badaru Abubakar, wanda ya fara da yin bayani a kan yadda suka tunkari matsalar, bayan sun karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.