Ana binciken lalata da dalibai a jami'ar Kaduna

Bayanan sautiKASU Sex 4Grades

Mahukuntan Jami'ar jihar Kaduna sun sanar da matakin dakatar da d'aya daga cikin malamansu, bisa zargin neman yin lalata da dalibai.

Rahotanni sun ce shekaran jiya ne wata daliba ta gudanar da zanga-zangar mutum d'aya, inda ta zargi jami'ar da zama mafaka ga wanda ake zargi da aikata lalata da dalibai.

Mataimakin shugaban sashen kula da harkokin dalibai a Jami'ar jihar Kaduna, Dr Tukur Abdulkadir ya ce tuni bincike ya yi misa kan zargin.

Ku latsa alamar lasifika dan sauraron sautin muryar.