Zaben 2019: Hotunan wasu zababbun gwamnonin Najeriya

BBC Hausa ta tattaro maku hotunan wasu 'yan takarar gwamna da suka sami nasara a zabukan gwamnoni da aka yi a Najeriya ranar Asabar 9 ga watan Maris 2019.

Dapo Abiodun na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar jihar Ogun

Asalin hoton, Facebook / Dapo Abiodun

Bayanan hoto, Dapo Abiodun na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar jihar Ogun. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.
Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar Legas

Asalin hoton, Twitter / @jidesanwoolu ‏

Bayanan hoto, Babajide Sanwo-Olu na jam'iyyar APC ne zababben gwamnan jihar Legas. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.
Ben Ayade na jam'iyyar PDP ne zababben gwamnan jihar Cross River

Asalin hoton, Twitter / @Ben_Ayade

Bayanan hoto, Ben Ayade na jam'iyyar PDP ne zababben gwamnan jihar Cross River. Ya ci zaben ne a karo na biyu.
A Gombe kuwa Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC ne wanda ya lashe zaben gwamnan jihar

Asalin hoton, Facebook / Inuwa Yahaya

Bayanan hoto, A Gombe kuwa Inuwa Yahaya na jam'iyyar APC ne wanda ya lashe zaben gwamnan jihar. Ya doke Sanata Bayero Nafada wadanda duk suka nemi takarar a karon farko.
Abubakar Sani Bello zababben gwamnan jihar Neja

Asalin hoton, Twitter / @GovNiger

Bayanan hoto, Abubakar Sani Bello na jam'iyyar APC ne ya lashe zaben gwamnan jihar Neja. Ya yi nasara ne a karo na biyu.
Sai kuma jihar Kwara inda Abdulrahman Abdulrazaq na APC ya sami nasara a zaben gwamnan jihar

Asalin hoton, Twitter / @RealAARahman

Bayanan hoto, Sai kuma jihar Kwara inda Abdulrahman Abdulrazaq na APC ya sami nasara a zaben gwamnan jihar. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamnan jihar.
David Nweze Umahi dan jam'iyyar PDP shi ne zababben gwamnan jihar Ebonyi

Asalin hoton, Facebook / David N Umahi

Bayanan hoto, David Nweze Umahi dan jam'iyyar PDP shi ne zababben gwamnan jihar Ebonyi. Wannan ne karo na farko da ya zama gwamna.
A jihar Jigawa Muhammadu Badaru na APC ne zababben gwamnan jihar

Asalin hoton, Facebook / Muh Badaru

Bayanan hoto, A jihar Jigawa Muhammadu Badaru na APC ne zababben gwamnan jihar. Badaru ya yi nasara ne a karo na biyu.
Mallama Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ne zababben gwamnan jihar

Asalin hoton, Twitter / @El-Rufai

Bayanan hoto, Mallama Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna ne zababben gwamnan jihar
A jihar Oyo kuwa, Seyi Makinde na PDP ne ya lashe zabenn gwamna a jihar

Asalin hoton, Twitter / @SeyiMakinde

Bayanan hoto, A jihar Oyo kuwa, Seyi Makinde na PDP ne ya lashe zabenn gwamna a jihar
A jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben mukamin gwamnan jihar

Asalin hoton, Facebook / Udom Emmanuel

Bayanan hoto, A jihar Akwa Ibom Mista Udom Emmanuel na jam'iyyar PDP ne ya lashe zaben mukamin gwamnan jihar