Kalli yadda guragu suka yi gasar rawa a Kano

Bayanan bidiyo, Kalli yadda guragu suka yi gasar rawa a Kano

Wata kungiya mai suna Matalison Welfare Foundation ta shirya wa wadansu guragu gasar rawa a Kano a ranar Alhamis.

An shirya gasar rawar Hip Pop din ne a wani bangare na bikin bai wa guragun kyaututtuka.

An kuma ba wadanda suka yi nasara a gasar kyaututtuka da kekunan guragu da sauransu a wani kokari na rage barace-barace.