Kalli yadda aka mamaye ofishin MTN kan 'muzgunawa' ma'aikata

Masu zanga-zangar de ke samun goyon bayan kungiyar kwadago ta Najeriya, sun mamaye ofisoshin kamfanin na Afirka ta Kudu a sassan kasar da dama.

Mambobin kungiyar kwadago na rike da kwallaye a zanga zangar nuna adawa akan yadda kamfanin MTN ya ke yi wa ma'aikata a Kano
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na kungiyar kwadago ta Najeriya, sun mamaye ofisoshin kamfanin wayar salula na MTN na Afirka ta Kudu a sassan kasar da dama.
'Yan kungiyar kwadago da ke zanga zanga
Bayanan hoto, Uwar kungiyar kwadagon kasar ce, wato NLC ta umurci `ya`yan nata da su dauki wannan matakin, sakamakon zargin da take yi cewa kamfanin sadarwar na zaluntar ma`aikatansa
Kungiyar ta nemisu kan suka yi zanga zanga a gaban ofishin kamfanin MTN
Bayanan hoto, Tun da asubahin fari zakara ya baiwa `yan kwadagon sa`a da su da gamayyar kungiyoyin farar-hula suka dunkule da nufin taron dangi, sannan suka mamaye babban ofishin MTN da ke Kano
Zanga-zangar nuna rashin jin dadi da kamfanin MTN
Bayanan hoto, `Yan kwadagon dai na zargin kamfanin MTN din ne da maida ma`aikatansa karan-kada-miya, suna rike masa kaho yana tatsa, kuma bayan sun tara masa arziki, sai ya sa kafa ya take musu hakkokinsu
Zanga zangar nuna rashin jin dadi da kamfanin MTN
Bayanan hoto, Wani kwali da wani ya rike da ke cewa babu wani da ke da hakkin bautar da mu a cikin kasarmu
Zanga zangar nuna rashin jin dadi da kamfanin MTN
Bayanan hoto, Sai dai kamfanin MTN a nasa bangaren, ya bayyana cewa `yan kwadagon sun jahilci yadda yake gudanar da harkokinsa ne, amm duk da haka za su sasanta
Wasu jami'an kungiyar kwadago
Bayanan hoto, A watan Oktoban bara ma, wannan batun tauye hakkin ne ya sa `yan kwadagon suka mamayi wasu rassan kamfanin MTN din a Najeriya, inda kamfanin yayi alkawarin sauya hali