Turkey: An bayar da belin 'yan jarida biyu

Asalin hoton, EPA
Wata kotu a Turkiyya ta bayar da belin wasu 'yan jarida biyu wadanda su kai aiki da jaridar adawa kuma wadanda a ka tsare sama da shekara guda.
A na zargin Babban editan Jaridar Cumhuriyet, Murat Sabuncu da wakilin jaridar Ahmet Sik da wasu abokan aikinsu da goya wa kungiyoyin ta'addanci baya.
'Yan jaridar dai sun musanta zargin. Haka kuma a na tsare da shugaban kamfanin da ke buga jaridar Akin Atalay kusan kwanaki dari biyar.
Kungiyar Reporters Without Borders da ke fatutikar kare 'yan jarida a duniya ta yi Allah-wadai da shari'ar kuma ta yi kira da a yi watsi da zargin.







