Babu wanda zai iya gadona nan kusa - Usain Bolt
Zakaran wasannin Olympic sau takwas a bangaren tsere Usain Bolt ya ce dole ne masu shan magungunan kara kuzari su daina shansu, in ba haka ba, wasannin motsa jiki za su daina armashi. Usain Bolt yana shirin yin ritaya bayan gasar zakaru da za a yi a watan Agusta.