Hotunan zanga-zangar 'matsin tattalin arziki' a Nigeria

Hotuna daga wasu manyan biranen Nigeria kan zanga-zangar da aka gudanar ranar Litinin a kan matsin tattalin arzikin da 'yan kasar ke fuskanta.

Masu zanga zanga
Bayanan hoto, Daruruwan mutane ne suka hallara a wasu manyan biranen Najeriya don gudanar da zanga-zanga kan matsin tattalin arzikin da kasar ta tsincin kanta a ciki
Masu zanga-zanga
Bayanan hoto, Kungiyar kare hakkin fararen hula ta Enough is Enough ce ta jagoranci zanga-zangar
Manenema labarai da wasu masu zanga zanga
Bayanan hoto, Kafafen yada labarai da dama sun halarci wuraren da aka gudanar da zanga-zangar, wadda a baya wani fitaccen mawaki 2face Idibia ne ya so jagorantarta
'Yan sanda
Bayanan hoto, Da farko dai jami'an 'yan sandan da aka zuba a birnin Lagos sun fi masu zanga-zangar yawa, amma daga bisani mutane sun karu har yawansu ya kai daruruwa.
kyalle mai dauke da sako
Bayanan hoto, Daga bisani mawaki 2face ya fasa yin zanga-zangar saboda barazanar da 'yan sanda suka yi ta kama shi, abin da ya sa wasu ke ganin zanga-zangar ba ta yi tasiri ba
Wani kyale da ke dauke da sakon da ke nuna goyon baya ga shugaba Buhari
Bayanan hoto, Wasu magoya bayan shugaba Buhari ba su yi na'am da zanga-zangar ba, don haka su ma suka fito don nuna gamsuwa da yanayin mulkin shugaban
Masu zanga zanga a birnin Lega
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar sun ce sun fito ne domin nuna damuwa a kan al'amuran da suke damun jama'a musamman hauhawar farashin kayayyaki.
Kwaleyen da wasu masu adawa da zanga zanga suka rike
Bayanan hoto, Wasu masu goyon bayan shugaba Buhari na dauke da kwalaye da aka rubutu 'Mun yi farin cikin kwato Sambisa da sojojin Najeriya suka yi'.